Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Yadda Ake Bude Sabon Adireshin Email Na Gmail a Wayar Hannu

Wallafan June 23, 2018. 6:20pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

Kirkira ko bude sabon adireshin Email abu ne mai sauki. Manhajar Gmail na kamfanin Google shi ne ke bada daman mallakan adireshin Email cikin sauki a wayar hannu. Idan kana amfani da 'browser' na waya kaman Opera mobile ko OperaMini ne, to kawai bi wadannan matakan guda 6 domin mallakan sabon adireshin ka na Email a Gmail:

(1) Da farko ka shiga www.gmail.com . Za ka ga wajen da aka sa 'New to Gmail? It's free and easy. Create account'. To sai ka danna 'Create account'.

(2) Zai budo maka wajen da za ka zabi sunan kasar ka. (country) da kuma wajen da za ka rubuta lambar wayar ka. To a wajen 'choose country', za ka ga 'change' sai ka danna shi.

Zai jero maka haruffa, sai ka zabi harafin da sunan kasar ka ya fara da shi. misali, 'N' idan a Nigeria ka ke ko Niger.

Bayan ka zabi sunan kasar ka, zai dawo da kai wajen da za ka saka lambar wayar ka. To sai ka dan yi kasa kadan, sai ka rubuta lambar wayar da ka ke kan amfani da shi a wayar ka a yanzu. Sai ka danna 'Next'.

(3) Za su aiko sakon SMS zuwa ga lambar wayar da ka sa, cikin yan mintunan da basu wuce 15 ba. Sai ka dan jira kadan, da zaran sakon ya shigo, sai ka je inbox na wayan ka, ka bude. A cikin sakon, za ka ga wani adireshi (link), sai ka latsa wannan link din. Ko kuma ka kwafe shi, sai ka je browser din ka, ka shiga ta ciki.

(4) Bayan ka latsa link din, ya bude, za ka ga wani fom da za ka cike sunan ka (first name), sunan mahaifi (last name) ranar haihuwa (date of birth), da kuma jinsi (gender). Bayan ka cike, sai ka danna 'Next'.

(5) Zai budo maka wajen da za ka zabi 'Username' din ka wato sunan da zai zamo adireshin Email din ka. Za ka ga sun baka wasu misalan sunayen adirishin da za ka iya zaba a kasa. Idan kuma wani daban ka ke so, ba daga cikin wadannan da suka baka ba, to sai ka rubuta wanda ka ke so. Da ka rubuta sai ka danna 'Next'. Amma idan akwai wani mai irin wannan sunan, to za su ce bai karbu ba, sai ka sake canza wani.

(6) Zai budo maka wani shafi da za ka saka mabudin ka na sirri (password). Sannan ka sake maimaita shi a kasa (retype password). Sai ka danna 'Finish'. Shi kenan! Ka gama bude sabon adireshin E-mail din ka na Gmail!

Haka kuma, za a iya yin rejistan sabon 'account' na Gmail din ta hanyar bin wannan adireshi: https://accounts.google.com/SignUp.

Idan a wayar Android ne, ko kuma iPhone, ga yadda za a kirkiri sabon 'account' na Email din ta hanyar App na Gmail, cikin sauki:

(1) Idan baka da manhajar wato App na Gmail din a wayar ka, to sai ka shiga App Store idan wayar iPhone ne, ko kuma Google Play Store idan a wayar Android ne, domin saukarwa.

iPhone — Tabi akwatin bincike wato 'Search', sai ka rubuta 'gmail', sai ka zabi gmail daga jerin da za ka gani. Sannan sai ka latsa 'GET' da ke bangaren dama na Gmail din, sai ka shigar da "Apple ID password" din ka ko "Touch ID".

Android — Tabi akwatin 'search' sai ka rubuta 'gmail'. Zabi manhajar na Gmail, sai ka latsa "INSTALL", kuma ka latsa "ACCEPT".

Idan kuma kana da manhajar na Gmail a wayar ka to shi ke nan, mu je zuwa mataki na gaba.

(2) Bude app din, duba cikin jerin apps na 'menu' din wayar ka, za ka gan shi, sai ka tabo shi domin budewa. Idan ya budo, za ka ga bangaren shiga wato 'Sign In' ne idan ba a taba shigar da wani 'account' din ba kenan, a wayar. Idan ka duba abubuwan zabi dake bangaren hagu, za ka ga 'More options' ko kuma 'Accounts' sai ka latsa shi. Sannan za ka ga 'Add Account' ko kuma 'Create Account' sai ka latsa shi.

(3) Zai budo maka wajen da za ka rubuta sunan ka (first name) da kuma wajen da za ka rubuta sunan mahaifi (last name). Bayan ka rubuta, sai ka latsa maballin 'Next' don zuwa ga mataki na gaba.

(4) Zai budo maka wajen da za ka shigar da 'Basic information' wato wajen da za ka shigar da ranar haihuwan na (date of birth) da kuma jinsi (gender). Bayan ka shigar sai ka latsa 'Next' don zuwa ga mataki na gaba.

(5) Zai budo maka wajen da za ka rubuta 'Username' din da kake so. Wato taken da zai kasance a adireshin Email din ka, kafin '@gmail.com'. Wajibi ne ya kasance wani suna ko taken da babu mai irin sa. Idan akwai mai irin 'Username' da ka rubuta, to zai nuna maka cewan akwai mai irin shi, ka canja wani daban. Bayan haka sai ka latsa 'Next' don zuwa ga mataki na gaba.

(6) Zai budo maka bangaren kirkiran kalman sirri wato 'Password'. To sai ka rubuta duk kalma ko alamomi da haruffa ko lambobin da ka zaba a matsayin 'Password' din ka, wanda ba za ka mance da shi ba. Sannan akwai kuma wajen da za ka sake maimaitawa (confirm password). Sannan sai ka latsa 'Next'.

(7) Zai budo maka wajen da za ka shigar da lamban wayar ka (phone number). To sai ka shigar da lamban wayar da za ka iya karban sakon SMS da shi. Sai ka latsa 'Next'.

(8) Zai budo maka wajen da za ka latsa 'Verify' domin tantance lamban wayar da ka shigar. Za su aiko da sakon SMS zuwa ga lamban wayan domin tabbatar da cewan mallakin ka ne. To sai ka je ka budo sakon SMS din wanda ya zo daga Google, za ka ga wasu lambobi guda shida (six digit PIN number) sai ka kwafo su, ka sanya su a wurin da aka sa 'Enter code'. Sai ka latsa 'Next'. Zai iya yuwuwa kuma ka tsallake wannan matakin ta hanyar zaban 'Skip' tun a baya.

(9) Za ka ga wajen da za ka latsa don nuna alaman amincewa da dokoki da ka'idojin Google wato 'I Agree'. Sannan sai ka latsa 'Next'.

(10) Shi ke nan! Sabon Account' din ka na Gmail ya budu. Za ka ga ya budo maka bangaren 'Inbox' na sabon Email din ka.

Idan aka yi rajistan, ba kawai adireshin Email kadai za a samu ba. Yin rajistan zai baka daman amfani da duk manhajojin kamfanin Google. Idan ana bukatan karin bincike da bayani game da bude sabon 'account' na Gmail din cikin harshen turanci to za a iya samu a wannan adireshi: https://support.google.com/mail/answer/56256?hl=en


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 19 a kan "Yadda Ake Bude Sabon Adireshin Email Na Gmail a Wayar Hannu"


Babu hoto28-01-2019
sulaiman

aslm


Babu hoto05-06-2019
MASAUD

Allah yasaka


Babu hoto07-09-2019
MUDANSIR

SULE


Babu hoto07-09-2019
MUDANSIR

SULE


Babu hoto07-09-2019
MUDANSIR

SULE


Babu hoto07-09-2019
MUDANSIR

SULE


Babu hoto23-01-2020
abubakar yusuf

Wajen sukuriti danakasansa


Babu hoto07-09-2020
Aliyu

Mun gode


Babu hoto11-09-2020
amutujugafap

http://mewkid.net/when-is-xuxlya/ - Amoxicillin 500mg Amoxicillin Online lcl.xvij.ahmadbala.zamaniweb.com.xhc.wv http://mewkid.net/when-is-xuxlya/


Babu hoto11-09-2020
elezoqsu

http://mewkid.net/when-is-xuxlya/ - Amoxil Dose For 55 Pounds Amoxil jfq.qjpm.ahmadbala.zamaniweb.com.xip.fe http://mewkid.net/when-is-xuxlya/


Babu hoto11-10-2020
ufetisifen

http://mewkid.net/when-is-xuxlya/ - Amoxicillin 500mg Capsules Amoxicillin Online bst.gkwf.ahmadbala.zamaniweb.com.cmm.mx http://mewkid.net/when-is-xuxlya/


Babu hoto11-10-2020
okacekop

http://mewkid.net/when-is-xuxlya/ - Amoxicillin Online Amoxicillin 500 Mg xhy.ugrm.ahmadbala.zamaniweb.com.wxs.qc http://mewkid.net/when-is-xuxlya/


Babu hoto28-10-2020
Mahmud sabo waziri

Rubuta sharhin a nan...


Babu hoto10-11-2020
urigevutejg

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Amoxicillin Without Prescription Amoxicillin 500 Mg gsv.nwtz.ahmadbala.zamaniweb.com.uon.zg http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto10-11-2020
uzhuazos

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Buy Amoxicillin Buy Amoxicillin nlj.ednz.ahmadbala.zamaniweb.com.qiz.ec http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto10-11-2020
awfavulin

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Amoxicillin Amoxicillin 500 Mg csh.jmmo.ahmadbala.zamaniweb.com.rjv.tc http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto01-01-2021
nym200276flebno

mns200276rttyneg vb4gDyM CtEM JmnqySE


Babu hoto01-01-2021
nam200276flebno

mes200276rtjuny BCBzMBU 5Rmt m1gzyky


Babu hoto22-02-2021
muhammad nagane

Allah yasaka maka

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka