Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Wakar Gwanin Da Muke So

Wallafan November 20, 2018. 9:20am. Na Ahmad Bala. A Sashin Rubutattun Wakoki Na
http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/43095338_360143291423177_1565409856511131077_n.jpg

Ina masoya Manzo
Ga lokacin nan ya zo
Da za mu karo kwazo
A yabon gwanin da muke so

Rabi'ul Auwalu kenan
Watan da mai hasken nan
Ya haskake duniyan nan
Har ya zam gwanin da muke so

A hidiman sa kar mu yi latti
Mu yabe shi kowane minti
In zuciya ta yi datti
Yabon sa kan zama soso

Shi suna na masoyi
Ko ambaton shi ake yi
Sai zuciya ta yi sanyi
Don ta ji wanda ta ke so

Ga wanda ba shi da aibi
Mahmudu mai kyan dubi
Tsirrai zuwa dabbobi
Sun nuna shi fa suke so

Ga shugaban iya mulki
Mai kyan hawa kan doki
Ga kyan kalaman baki
Gare shi wanda muke so

Ga shugaban shugabanci
Matattarar adalci
Da tuno shi na bar kunci
Na tsunduma tafkin so

Shi ne ya kawo canji
A garuruwa har daji
Ya haskaka mana kirji
Har ya zam gwanin da muke so

Ina kira ga masoya
Ku zo duk mu hau hanya
Hanyar Baban Rukaiya
Wannan gwanin da mu ke so


© Ahmad Bala
12/03/1440 A. H.

Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Wakar Gwanin Da Muke So"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka