Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Tsokaci Game Da Sahihancin InksNation

Wallafan September 10, 2020. 6:35pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

Gabatarwa

Da sunan Allah mai rahama Mai jin kai. Na samu sakonnin tambayoyi game da sahihancin wannan kamfani na InksNation daga mutane da dama wadanda ke son su tabbatar da sahihancin sa kafin su saka kudin su. Don haka ne na zauna na dan yi bincike game da lamarin. Kuma na yanke shawaran yin wannan bayanin domin amfanin al'umma baki daya. Amma da farko sai na fara da bayani a game da fasahar 'cryptocurrency' domin sai an fahimce shi ne sannan za a iya tantance sahihancin kamfanonin da ke hada-hadar sa.

Mene ne Crypto currency (kudin krifto)?

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/1827866-879321743.jpg

'Crypto currency' wanda na fassara shi da 'kudin krifto', wani fasaha ne wanda ke matsayin kudi amma na lataroni ('digital currency'). Kudi ne da ake iya amfani da shi wajen saye da sayarwa ta hanya mafi tsaro a duniyar intanet. Akwai nau'ukan kudin krifto daban-daban amma na farko kuma mafi shahara daga ciki shi ne Bitcoin, wanda aka kirkire shi a shekarar 2009.

Gudanar da kasuwanci tare da kudin krifto irin su Bitcoin da Ethereum abu ne mai kyau da inganci. Kasancewar kudin krifto na aiki ne bisa wani tsari na fasaha wanda ake kira 'Blockchain', yana bada daman kauce wa hatsarurruka da dama a yayin gudanar da cinikayya a duniyar intanet. Haka kuma ana samun alheri sosai a harkar cinikayyar kudin na krifto. Wanda hakan ne ya sa fasahar ya samu karbuwa matuka a fadin duniya. Sai dai kuma a duk lokacin da aka ce an fito da wani sabon fasaha, to lallai sai an samu wasu gurbatattun mutane masu kokarin kawo rashin gaskiya cikin abin domin cin ma wata manufa tasu.

Ana yawan samun kamfanoni 'yan sabon-shiga masu kokarin yin gogayya da Bitcoin da makamantan sa. Wanda za su fito tare da sabon sulallan kudin krifton su, abin da akan ce ma 'Initial Coins Offering' ko ICO a turance. Amma kuma babu ingantaccen tsarin kariya daga asara ga masu zuba dukiyar su wajen mallakan shi. Don haka daga bisani idan kamfanin ya gaza, sai mutanen da suka zuba dukiyar tasu su kwan ciki.

Duk da kasancewan a 'yan shekarun baya-bayan nan, mahukunta daban-daban a fadin duniya sun rika kokarin kawo dokokin da za su tsare fasahar ta hanyar fito da tsarin mayar da kudaden krifto zuwa kadarori ('assets'). Ko kuma tilasta amfani da tsarin zuba hannun jari ('investment') ga sababbin kamfanonin da suka fito da sabon sulallan kudin krifto (ICO). Sai dai duk da irin wannan tsare-tsaren da wasu mahukunta kan yi kokarin sanyawa a matsayin dokar da za ta inganta fasahar mu'amala da kudin krifto, har yanzu ana ci gaba da samun baragurbin kamfanonin da ke fakewa da shi su cuci jama'a.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/picture2-429x315.png

A bisa kididdigan CipherTrace, idan aka kwatanta da shekarar 2018, asarar da masu zuba dukiyar su a harkar kudin krifto ke yi ya karu da kashi 533% a cikin watanni 12 kacal, inda asarar ya kai kusan na dala biliyan 4.5 a shekarar da ta gabata.

Ina sahihancin InksNation?

Don gudun fadawa tarkon kamfanonin da ke cutar mutane a harkar na kudin krifto, mutane da dama sun rika sanya shakku a kan lamarin wani kamfani mai suna iBSmartify Nigeria Ltd wanda aka fi sanin sa da sunan manhajar yanargizon nasa, wato InksNation.io. InksNation ya fito da kudin krifton da ya sa wa suna 'Pinkoin' kuma yana ikirarin cewar tsarin fasahar 'Blockchain' din sa mai taken 'InksLedger' zai iya kawar da talauci a kowace kasa cikin kasa da watanni 9.

Sau da yawa karancin ilimin abu da kuma rashin zurfafa bincike ke sa mu fada tarkon 'yan damfara. Don haka ga wasu abubuwa guda 10 wanda na lura sannan na ke fatan kuma za ku lura da su a game da InksNation:

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/_20200910_185403.png

1. InksNation ba shi da rajista da hukumar SEC

Na yi bincike a shafin yanargizon hukumar da ke sa ido a kan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasa wato 'Security and Exchange Commission (SEC)', inda na gano cewan InksNation ba shi cikin kamfanonin da suka yi rajista da hukumar na SEC.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/tmp-cam-3360573677393215692.jpg

2. Hukumar SEC ta yi gargadi a kan InksNation

Sun fitar da gargadin ne a shafin yanargizon su da kuma shafin su na twitter, inda suke cewa:

"iBSmartify tare da haramtacciyar hajar da suke tallatawa  ba su da rajista da mu kuma ba su a karkashin kulawar hukumar mu. Don haka ana gargadin daukacin al'umma da cewan duk wanda ya ke hulda da su ko makamantan su to ya kwana da sanin cewan yana cikin ganganci". - shafin SEC

3. InksNation basu mayar da martani ba

Har zuwa wannan lokaci, InksNation basu ce wani abu a game da batun da SEC ta yi a kan su ba.

4. Ikirarin bayar da N120,000 duk wata

Har zuwa wannan lokacin da nake wannan rubutun, ban samu labarin wani dan Najeriya, mamba na InksNation din, wanda ya ce ya karbi N120,000 din da suka alkawarta cewa za su rika badawa duk wata ba.

5. Babu cikakken bayani game da manufar su

Suna ikirararin cewan manufar su shi ne kawar da talauci a doron kasa. Sun ce suna amfani da fasahohin 'Blockchain' da 'Artificial Intelligence' da 'Extended Reality' da Kuma 'Quantum computing'. Amma ba su yi bayanin ta yadda suke amfanin da su ba. Shin ko so suke su ruda mutane saboda karancin ilimin da ake da shi a kan wadannan fasahohin? Oho! A bangare guda kuma suna ikirarin cewa dan adam shi ne babban kadara da suke amfani da shi wajen cin ma wannan manufar kawar da talaucin. Amma sai dai ba su yi bayanin ta yadda za su yi hakan ba. Bisa ga dukkan alamu dai, za su ci gaba da samun makudan kudade daga hannun dubban mutanen da ke ci gaba da yin rajista da su, ido rufe, a halin yanzu.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/tmp-cam-1823816703619787355.jpg

6. Basu da wasu dokoki da ka'idoji ('Terms and Conditions') a shafin su a halin yanzu

Idan ka duba bangaren 'Terms and conditions' na shafin, za ka lura cewan rubutun da ke wajen iri daya ne da rubutun da ke bangaren bayanan tsarin tsare sirri wato 'Privacy Policy' na shafin. Duk da cewa taken yana nuna 'Terms and conditions'. Ma'ana dai kaman kawai sun kwafo abin da ke wancan bangaren ne suka ajiye a nan ('copy and paste') don basu da wasu dokoki da ka'idojin da za su bayyana wa mutane.

7. Wata zance maras tushe daga bakin wanda ya kafa kamfanin

Mallam Omotade-Sparks Amos Sewanu shi ne wanda ya kirkiro InksNation. A watan Maris din da ta gabata ya fito a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin twitter na kamfanin InksNation din, yana cewa "ko ku yarda ko kar ku yarda, borkonu ('yaji') ya na maganin cutar korona". Kuma ya yi wannan batu ne a daidai lokacin da hukumomi da sauran jama'a ke ta kokarin yaki da labaran karya game da cutar a kafafen sadarwa.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/tmp-cam-2327819977682823472.jpg

8. Sun saka hoton "Ubangiji" a shafin

Idan kuka duba bangaren "Team" na shafin nasu za ku ga wani hoton "Ubangiji" da sunan "Elohim JahGah" tare da sanya taken "God the Trinity Trustor & Grantor" a karkashi. Har ma suka sanya mahada wanda za a iya bi a tuntube ubangijin a shafukan sada zumunta. Sai dai mahadan fanko ne, idan ka latsa babu shafin da ke budewa. Wannan ya sa wasu ke dauka cewan InksNation din nan sun zo da tsabar "rainin hankali".

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/tmp-cam-8568338547790291006.jpg

9. InksNation ba shi da rajista da kungiyan SIBAN

Wata kungiya ta masu ruwa-da-tsaki a harkokokin kudin krifto da fasahar 'Blockchain' a Najeriya mai suna 'Stakeholders In Blockchain technology Association of Nigeria' (SIBAN) ta bayyana a shafin ta cewan InksNation ba shi da rajista da kungiyan. Kuma ta yi gargadi tare da cewan "Pinkoin yaudara ne, don haka a kaurace ma sayen sa" a shafin ta na twitter.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/siban-482x420.png

SIBAN dai kungiya ce da ta shahara wajen kokarin ta na wayar da kan al'umma a game da harkokokin kudin krifto da fasahar 'Blockchain' a Najeriya. Za ku iya duba cikakken bayanin da kungiyar ta fitar a shafin ta na yanargizo.

10. Kariyar da InksNation ke da shi daga hukuncin dakatarwa

Duk da kasancewan wasu hukumomi sun gano rashin sahihancin wannan kamfani na InksNation, abu ne mai wahala a iya daukan matakin shari'a wajen dakatar da su. Dalili na farko shi ne: InksNation sun fake ne a karkashin inuwar kasuwancin fasahar 'Blockchain' wanda shi kuma kasuwanci ne ingantacce wanda duk duniya an amince da shi, kaman yadda na yi bayani a farko. Wannan ne ma ya sa suke da rajista tare da hukumar CAC a matsayin halastaccen kamfani. Dalili na biyu kuma: har yanzu gwamnati ba ta da wasu dokoki ko tsare-tsare na musamman don sa ido a harkokin kudin krifto da fasahar na 'Blockchain'. Sai dai wannan a iyakacin sani na ne kawai. Idan kuwa hakan ne, to daga yanzu har zuwa wani lokaci mai tsawo, InksNation za su ci gaba da cin karen su babu babbaka.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/pinkoin-scam.jpg

Fadakarwa

  • Baya ga InksNation, akwai wani "Forsage" da kuma "Ethereum Million Money" da sauran ire-iren su wanda duk alamomi sun nuna rashin sahihancin su.
  • Najeriya ita ce ke kan gaba wajen hada-hadar kudin krifto a Afrika gaba daya, haka kuma Najeriyar ce sahun gaba a wajen damfara da cuta a fannin. Don haka ya zama wajibi mu rika bambancewa tsakanin nagari da na banza.
  • Duk da kasancewan al'umma na cikin wani yanayi wanda ya sa jama'a da dama ke neman hanyoyin samun kudi ido rufe, lallai sai mun yi taka-tsan-tsan domin kada garin neman kiba a samo rama. Kada mu manta masu iya magana kan ce "kwadayi mabudin wahala ne".
  • Akwai sahihan hanyoyin samun kudi ta hanyar kasuwancin kudin krifto da ma suaran hanyoyi a yanargizo daban-daban wanda za mu iya cin moriyar su ba tare da wata fargaba ba, idan muka jajirce muka yi aiki tukuru. Kuma insha'Allah, da sannu zan yi kokarin fito da su don masu ra'ayin sanin su.
  • Yana da kyau komai za mu yi a rayuwa, mu nemi ilimin sa tukuna.

Kammalawa

Ni bana goyon bayan shiga ko hulda da InksNation a halin yanzu, bisa ga dalilan da suka bayyana gare ni. Kuma a sani cewan, wannan rubutun na yi shi ne don ilimantarwa da fadakarwa kawai. Kowa na da damar sa na amincewa ko rashin amincewa da wani abu, bisa ga dalilai ko hujjojin da suka bayyana gare sa. Don haka duk wanda ya ga cewan lallai shi ya gamsu da tsare-tsare da manufar InksNation din a halin yanzu, to sai dai in ce da shi "dabara ta rage ga mai shiga rijiya".

Bissalam! Ku kasance lafiya.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 11 a kan "Tsokaci Game Da Sahihancin InksNation"


Babu hoto10-09-2020
Abdurraheem Muhammad

A GASKIYA Muna Godiya Allah Yasaka da Alheri


Babu hoto12-09-2020
Kabiru Ahmda Datti

Allah yashiga tsakanin nagari da mugu


Babu hoto12-09-2020
Ahmad Bala

@Abdurraheem Muhammad, Ameen Ya Allah 🙏


Babu hoto12-09-2020
Ahmad Bala

@Kabiru Ahmda Datti, Ameen!


Babu hoto12-09-2020
Ali muhammad

Mungode, Allah yasaka


Babu hoto22-09-2020
Abdullahi Usman

na karanta tun daga farko har zuwa karshe kuma gaskiya na karu akan jawabin da kayi bama kadai Maganar inksnation ba har ma da kara wayar mun kai da kayi akan kowani manhaja kafin ka fara mu'amala da shi ka wayar muna da Kai akan wasu bincike kafin mu fara mu'amala da wani manhaja nagode sosai da sosai Allah ya karo ilimi mai anfani nagode sosai


Babu hoto29-09-2020
Abubakar babangida

Toh Gaskiya kam mudai mun riga munyi register wlh amma Kara kiyaye gabanmu da iren shiga Wannan abu


Babu hoto26-10-2020
Gaddafi saidu ahmad

Mungode allah ya shiga tsakanin nagari da mugu


Babu hoto26-10-2020
Mutar salisu kanya babba

Allah ka karemu daga makircin yahudawa


Babu hoto05-11-2020
Aisha yusuf

Mudai munriga da munyi saidai allah yakare nagaba


Babu hoto23-12-2020
Abuabdul communication

Munagodiya gamida Fatan alkhairi Allah Yakarawarayuwa albarka

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka