Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Shin Ko Akwai Bukatar In Mallaki Shafin Yanar Gizo Don Kasuwanci Na?

Wallafan June 23, 2019. 6:48pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

"Shin Ko Akwai Bukatar In Mallaki Shafin Yanar Gizo Don Kasuwanci Na?"

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/06/1/need-website-small-business.png

Amsar wannan tambayar zai iya kasancewa "Eh" kuma zai iya kasancewa "A'a". Mai kasuwancin ne kawai zai iya bai wa kan sa amsa.

Kai kadai za ka iya ba kan ka amsa. Sai dai a yayin kokarin amsa tambayar, ya kamata ka sani cewan shi dai shafin yanar gizo yana da amfanoni masu yawa, kuma shi hanya ne na sadarwa ba talla ba ne kaman yadda wasun mu da yawa sukan dauka. Idan kasuwancin ka ya kasance na iyakacin wasu mutane ne kalilan wadanda ke kusa da kai, kaman misali ya kasance abokan cinikayyar ka duk suna iyakacin unguwar ku ko layin ku ne, kuma ya kasance akwai tarin masu saye ko masu neman aikin ka da ke jirace, sannan kuma ya kasance duk kana iya sallaman kowannen su nan take ka samu ribar ka, to babu bukatar sai ka mallaki shafin yanar gizo don bunkasa wannan kasuwancin.

Amma idan ya kasance cewan kana da burin samar da hanyar da zata sadar da kasuwancin ka ga jama'an da ke nesa da na kusa baki daya, kuma hanyar da zai baka damar amsa tambayoyin da abokan cinikayyar ka za su so samun amsoshin su daga gareka, kuma hanyar da zai baka damar haduwa da sababbin abokan cinikayya, sannan kuma hanyar da zai baka daman shiga kasuwar duniyar intanet da kuma yin gogayya da sauran takwarorin kasuwacin ka, to mallakan shafin yanar gizo ya zama WAJIBI gare ka!

Shi shafin yanar gizo kaman wata mahanga ne inda mutane za su iya samun bayanai game da kasuwancin ka, kaman adireshin inda kasuwancin naka ya ke, da kuma aiyukan ko hajojin da ka ke dauke da su. Bugu da kari kuma, zai baka daman bayyana wa jama'a dalilan da suka sa kasuwancin ka ya fita daban da na saura. Sannan zai baka daman tallata sababbin aiyuka ko hajojin da kamfanin ka ke dauke da su. Kasancewan shi shafin yanar gizo ana sabunta shi ne akai-akai, kuma zai kasance wani matattara ko dandali wanda a nan ne abokan cinikayyar ka za su rika isar maka da bukatun su, ko tambayoyin su ko kuma shawarwari wanda wadannan duk sinadarai ne da za su bunkasa kasuwancin ka.

Shin kana bukatar karin bayani game da mallakan shafin yanar gizo don kasuwancin ka?

Tutube ni don mu tattauna, zan baka bayanai masu gamsarwa a kyauta!


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "Shin Ko Akwai Bukatar In Mallaki Shafin Yanar Gizo Don Kasuwanci Na?"


Babu hoto14-11-2020
labaseenho zanfo

ina buqatar mallakar shafin yanar gizo

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka