Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Kasidu a karkashin sashen: Rubutattun Wakoki Na (Rukuni na 1)

Hoton kasida

Wakar Gwanin Da Muke So

Wallafan November 20, 2018. 9:20am. Na Ahmad Bala. A Sashin Rubutattun Wakoki Na

Ina masoya Manzo Ga lokacin nan ya zo Da za mu karo kwazo A yabon gwanin da muke so Rabi'ul Auwalu kenan Watan da mai hasken nan Ya haskake duniyan nan Har ya zam gwanin da muke so A hidiman sa kar mu yi latti Mu yabe shi kowane minti In zuciya ta yi datti Yabon sa kan zama s...


Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComSababbin Kasidun Blog