Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Phishing: Yadda Hackers Ke Sace Bayanai a YanarGizo

Wallafan April 1, 2019. 4:37pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

Phishing wata hanya ce ta yaudara wanda 'yan dandatsa wato hackers suke bi wajen sace bayanan taskan mutane a intanet. Kaman bayanan taskan adireshin Email ko na Facebook ko na Bankin intanet da dai sauran su.

Yadda wadannan mayaudara ke yi shi ne, a misali - idan suna son su sace bayanan taskan ka na facebook don yin kutse ko kuma sace taskan gaba daya, da farko za su kirkiri wani shafin yanar gizo ne wato website na jabu, mai kama da facebook, sai su yi wa shafin ado da tsari da kala irin na facebook ta yadda duk wanda ya ziyarci shafin zai zata cewan ainahin shafin facebook din ne. Sannan kuma su kan sanya ma irin wannan shafin nasu na bogi adireshi mai kama da na facebook din. Misali, za su iya sanya wa shafin adireshi kaman haka: www•facebook-gold•cf

Da zaran sun kirkiri wannan shafi mai kama da facebook, to sun kirkiri tarko kenan, sai kuma su zo su fara neman wanda za su yaudara ya fada wannan tarkon nasu. Su kan yi amfani da WhatsApp ko Email ko kuma facebook wajen yada sakonnin su na karya da yaudara ga mutane, kaman haka:

"Mark Zuckerberg ya saye kamfanin WhatsApp a bara sannan kuma ya sanya manhajar na WhatsApp ya kasance sai an biya wasu kudi sannan za a samu daman ci gaba da amfani da shi. Don haka daga shekara mai zuwa za ku ga WhatsApp din ku ya daina aiki har sai kun biya wasu kudi. Amma an yi rangwame ga tsofaffin masu amfani da WhatsApp din ta yadda za su ci gaba da amfani da manhajar ba tare da biyan ko sisi ba. Domin samun wannan rangwame sai ka shiga www•facebook-gold•cf"

To haka za su kirkiri karya irin wannan su yi ta tura ma mutane. Har ma za ku ga wani lokaci a karshen sakon za su ce ka tura zuwa groups guda kaza, wai za ka ga WhatsApp din ka ya canja kala. To duk wannan karya ne. Abin da zai faru da zaran ka shiga wannan shafi nasu shi ne: za ka gan shi tamkar shafin shiga wato 'login page' na facebook. So suke ka sakankance cewan facebook din ne na gaske, har sai ka shigar da bayanan sirrin ka, kaman password. Ta yadda idan ka shigar da password din ka na facebook zai fado wajen su ne, inda daga nan kuma za su yi amfani da shi su shiga cikin taskan ka na facebook din don su rika wallafa wasu abubuwa marasa kyau, kaman hotuna na batsa, ba tare da sanin ka ba. Ko kuma ma su sace taskan facebook din naka gaba daya.

To wanan shi ake ce ma 'Phishing'. Kuma irin wannan hanya sukan bi su sace taskan adireshin Email, ko kuma ma mafi muni, su sace bayanan shiga shafin yanar gizon Bankin intanet din ka.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/04/1/phishing_img_victim.jpg

Ganin wannan ta'asar da irin wadannan miyagun mutane ke yi, na ga ya dace in yi wannan rubutu don ankarar da mutane. Domin sai ka fahimci hanyoyin da suke bi sannan za ka iya fahimtar yadda za ka kare kan ka.

Kalmar 'phishing' kalma ce ta turanci wadda idan kun lura ta yi kama da kalmar 'fishing' a wajen furuci, wato kama kifi. Wasu na ganin cewan hakan bai rasa nasaba da yadda wadannan miyagu kan aika sakonnin yaudara ga dimbin jama'a da nufin samun bayanan sirrin wanda tsautsayi ya rutsa da shi kaman dai yadda mai kamun kifi kan jefa komar sa da nufin kama kifi. Bincike ya nuna cewan mutum daya daga cikin mutane goma wanda aka aike wa irin wadannan sakonnin kan fada cikin tarkon.

Da yardan Allah, a rubutu na na gaba a wannan sashe zan kawo maku hanyoyin da mutum zai bi domin ya kubuta daga fadawa cikin tarkon wadannan miyagu, 'yan dandatsa, wanda su ke amfani da dabarar 'phishing' wajen sace bayanan mutane a yayin da suke mu'amala da intanet.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "Phishing: Yadda Hackers Ke Sace Bayanai a YanarGizo"

2019-04-22 07:03:44

123@#$%&

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka