Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Kalli Hotunan Bikin Maulid a Garin Zaria

Wallafan November 21, 2018. 10:22pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Hotuna

Kaman dai yadda kuka sani, a ranar talatar da ta gabata ne, wato 20 ga watan Nuwamban shekarar 2018 ya kasance dai-dai da 12 ga watan Rabi'ul Auwal na shekara 1440, ranar da musulmai a sassa daban-daban na duniya kan yi bikin zagayowan ranar haihuwan fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W.).

Na samu halartan fadan mai martaba sarkin Zazzau a wannan rana, kuma kasancewan daukan hoto na daga cikin aiyukan da na kan samu nishadin yi musamman ma a ranakun hutu irin wannan, ina tare da 'yar kyamara na, inda a yau na zo maku da tsarabar hotunan da na dauka na kadan daga cikin dubban mutanen da suka fito, maza da mata, yara da manya, suka yi zagaye a tsakiyar birnin na Zazzau don nuna murnar su da soyayyar su ga shugaban musulunci, Annabi Muhammad (S.A.W.).

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p1.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p2.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p3.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p4.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p5.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p6.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p8.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p9.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p10.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p11.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p12.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p12a.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p13.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p18.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p19.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p25.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p27.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/p16.jpg

Ma-sha-Allah! Muna fatan Allah Ya sa mu ga na shekaru masu zuwa lafiya. Kuma Allah Ya tabbatar mana da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali da kaunar juna a wannan kasa tamu Najeriya, Amin!

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/11/1/tmp-cam-109257150.jpg


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Kalli Hotunan Bikin Maulid a Garin Zaria"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka