Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Manhaja Mai Basira!

Wallafan November 24, 2019. 3:44pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo
http://zamaniweb.com/administrator/files/19/11/1/zamaniweb_manhaja_mai_basira.png

Bambancin wakilin suna wato "pronoun" wanda harshen Hausa ke da shi tsakanin sa da harshen English ya sanya masu fassara shafukan yanargizo ba sa iya yin fassara wanda ya dace da kowane jinsi (mace da namiji).

Misali: a English za a iya cewa "How are you?" ga kowane jinsi. Amma idan aka zo fassara shi zuwa Hausa sai an nemi sanin wane jinsi ne. Idan namiji ne sai a ce "Ya kake?". Idan ko mace ce sai a ce "Ya kike?".

Wannan bambanci na wakilin suna ya sa wasu masu fassara suke hakura su rika amfani da bangaren jinsi daya. Misali: sai ku ga a wasu shafukan yanargizon da aka fassara daga English zuwa Hausa, sai ku ga an rubuta "Ka shiga nan" ba tare da la'akari da mace ce ko namiji ne ke duba shafin ba. Ko kuma ku ga an sa "Ka/Kika". Duk wannan ana yi ne saboda ba a da hanyar samar da fasahar da za ta rika gano jinsin mai amfani da manhaja ko shafin yanargizo kai tsaye.

Mafita: - Manhaja mai basira

A karo na farko a duniyar fasahohin zamani, manhajar ZamaniWeb ya kawo mafita a kan wannan matsalar. Domin shi ba fassara shi aka yi daga turanci ba. Manhaja ne wanda aka kirkire shi da harshen Hausa ziryan. Sannan an kirkire shi tare da fasahar gano jinsin mai amfani da shi. Don haka idan jinsin mai amfani da shi namiji ne zai ce "Barkan ka da zuwa! Kirkiri sabon shafin yanargizon ka". Idan kuma jinsin mace ce zai ce "Barkan ki da zuwa! Kirkiri sabon shafin yanargizon ki". Idan kuwa aka shigar da wani bayanin da ba dai-dai ba, zai duba ya gani, idan jinsin mace ce zai ce "Abin da kika shigar bai yi dai-dai ba". Idan na namiji ne zai ce "Abin da ka shigar bai yi dai-dai ba".

Wannan kadan ne daga cikin basirar manhajar ZamaniWeb! 😎


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "Manhaja Mai Basira!"

2020-03-21 08:23:55

cerne bi orgie cerny sex klub lesbicky sex bideo parohac cerne zeny zdarma gay pornohub https://4jobar.com/hd-koika-kurva-fotka.html teen tesne kurva

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka