Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Kwamfuta Ko Na'ura Mai Kwakwalwa?

Wallafan September 10, 2020. 6:14pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Sababbin Kalmomin Hausa

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/tmp-cam-2562720620419624448.jpg

A gani na, fassara kalmar "Computer" zuwa "Na'ura mai kwakwalwa" maimakon "Kwamfuta" daidai ya ke da fassara kalmar "Qalamun" zuwa "Abin rubutu" maimakon kawai "Alkalami".

Har yanzu wasu 'yan jaridu, musamman ma a gidajen talabijin da rediyo, da masu rubuce-rubuce a kafofin sadarwa na amfani da "Na'ura mai kwakwalwa" a matsayin fassarar kalmar "Computer". Duk da kasancewan ba haka hausawan ke fadi ba a maganganun su na yau da kullum.

Ina ganin idan dai har muna so yaren Hausa ya ci gaba da bunkasa to wajibi ne mu rika yin fassara mai sauki ga sababbin abubuwa musamman ma a fannin kere-keren fasaha.

Shin mene ne tunanin ku a kan wannan??


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Kwamfuta Ko Na'ura Mai Kwakwalwa?"


Babu hoto12-10-2020
shuaibu muazu

wannan fassarar tayi dai-dai dacewa NA'URA MAI KWAKWALWA amatsayin COMPUTER.


Babu hoto12-10-2020
shuaibu muazu

wannan fassarar tayi dai-dai dacewa NA'URA MAI KWAKWALWA amatsayin COMPUTER.

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka