Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar Dan Arewa a Kan Harkokin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Game Da KadHack2018 Hackathon

Wallafan December 9, 2018. 10:26pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Harkoki Na

"Hackathon" sha'ani ne da ke hada masu ruwa da tsaki a harkar injiniyancin manhajar kwamfuta domin su yi amfani da kwarewar su wajen kawo sababbin kirkire-kirkire da za su kawo sauyi ko mafita a kan wasu matsaloli da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya.

KADHACK2018 Hackathon ne wanda kungiyar eHealth Africa a karkashin shirin GRID3 Nigeria tare da gwamnatin jihar Kaduna suka shirya, tare kuma da hadin gwiwar CoLab, a garin Kaduna.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k4.jpg

Daga cikin darurruwan mutanen da suka nuna sha'awar su na shiga wannan Hackathon, Allah Ya sa na kasance daya daga cikin mutum 30 da aka zaba domin gudanar da wannan gagarumin hackathon wanda irin sa na farko ne a jihar Kaduna.

A cikin mu 30 din nan akwai kwararru a kan injiniyancin manhaja wato "developers" wanda na kasance cikin su, akwai kuma kwararru a kan sarrafa bayanan kwamfuta wato "data scientists" duk daga sassa da kuma jihohi daban-daban na Najeriya.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k3.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k1.jpg

Manufan Kadhack2018 shi ne kirkiro sababbin fasahohin da za su kawo mafita kan wasu matsaloli a fannin kiwon lafiya da kuma ilimi.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k2.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k7.jpg

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k5.jpg

Mun gudanar da wannan hackathon cikin nutsuwa tare da nishadi. A karshen sha'anin wanda na iyakacin kwanaki uku ne, mun samu nasaran kirkiro sababbin manhajoji na waya da na yanar gizo da kuma na kwamfuta wandanda a ke sa ran za su kawo gagarumin sauyi kuma za su saukaka wa al'umma hanyoyin gudanar da wasu al'amura da dama a bangaren harkokin kiwon lafiya da kuma ilimi.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/12/1/k6.jpg

Ga duk mai son ganin wasu daga cikin manhajojin zai iya latsa nan domin dubawa a shafin Devpost.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Game Da KadHack2018 Hackathon"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Wane Ne Ahmad Bala?

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, wanda sha'awar sa a fannin fasahar sadarwan zamani ta kai shi ga koyar da kan sa ilimin sarrafa HTML da CSS da PHP da SQL da kuma JavaScript ta intanet, kuma har ya kware a kan su, ba tare da ya taba zama a cikin aji ya koyi wani darasi da ya danganci kwamfuta ko yanargizon ba. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni na fasahar sadarwan zamani, ya kirkiri manhajojin yanar gizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son duk wani abu da ya danganci kirkire-kirkire. Ku kasance tare da shi a twitter: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb, manhajar yanar gizo ne wato "web app" kuma "Internet platform" da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wato "website", a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika, don karfafa gwiwan yin amfani da fasahar sadarwan zamani, don samar da ci gaban nahiyar. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka