Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Facebook zai bude sabon ofishi a Najeriya

Wallafan October 6, 2020. 2:19pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/markzurk-in-lagos.png

Facebook ya sanar da fara shirye-shiryen kaddamar da sabon ofishin sa a birnin Legas a Najeriya. Ofishin shi ne zai kasance na biyu a Afrika, inda ofishin Facebook din na kasar Afrika ta kudu ya kasance na farko. Wannan labari na zuwa ne bayan shekaru hudu da kawo ziyarar shugaban kamfanin Mark Zurkerberg zuwa kasar ta Najeriya.

Zuwan Facebook Najeriya dai abu ne da ake ganin zai bayar da gagarumar gudun mawa wajen ci gaban harkokin fasaha a kasashen yammacin Afrika. Ana hasashen cewan sabon ofishin na Facebook zai fara aiki ne a tsakiyar shekara mai zuwa na 2021.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/10/1/facebook-office-780x405.jpg

Kididdaga a Najeriyar dai na nuni da cewan kimanin mutane miliyan 33 ke amfani da manahajar Facebook din a kowane wata. Inda kimanin 'yan kasar miliyan 16 kuma ke amfani da shi a kullum. Wanda hakan ne ya sa Najeriyar ta kasance kasa ta daya wacce ta fi kawo wa kamfanin na Facebook kudaden shiga a Afrika baki daya.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Facebook zai bude sabon ofishi a Najeriya"


Babu hoto06-10-2020
Baba Waziri

Gaskiya wannan labarin na bude ofishin facebook a nijeriya yayi matukar kyau ganin yadda yanzu ci gaban fasahar zamani yake.


Babu hoto14-04-2021
Janetrig

Hello, Download music private FTP: https://0daymusic.org MP3/FLAC, Label, LIVESETS, Music Videos, TV Series. Best regards, 0day MP3s

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka