Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Facebook Ya Kara Sabon Alamar 'Care'

Wallafan May 2, 2020. 8:05am. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

sabon-facebook-care-reaction.jpg

Facebook ya fito da sabon alama na nuna 'kulawa' wato 'care reaction' domin taimaka wa jama'a wajen nuna kulawa ga junan su. Kamfanin na facebook ya ce yana fatan wannan alama wanda ke nuna fuskar mutum rike da alamar zuciya, zai taimaki jama'a wajen nuna dankon zumunta ga 'yan'uwa da abokan su a wannan yanayi na annoba da duniyar ta ke ciki a halin yanzu.

A lokaci guda ne kuma, wani alamar da ke nuna bugun zuciya wanda facebook ya kira 'a beating heart' ya bayyana a manhajar Messenger na facebook din.

Wannan dai za a iya cewa sharan fage ne idan aka yi dubi da irin manyan sauye-sauye da kamfanin ke yunkurin fito da su a manhajar na facebook. Inda ko a kwankin baya ma kamfanin ya sanar da fara yakar labarun karya wanda jama'a ke yadawa game da cutar korona bairos, ta hanyar sanya sakon tunatarwa a 'News Feed' na duk wanda ya tura wani labari ko ya yi sharhi ko ya nuna alamar 'so' a kan wani labarin da bai inganta ba a game da cutar.

A bangare guda kuma, kamfanin na facebook ya bayyana cewa ya samu karin yawaitar masu amfani da manhajar tun bayan fitowar wannan annoba ta koronabairos a fadin duniya. Sai dai kuma facebook din ya bayyana cewa duk da kasancewar masu amfani da manhajar sun karu a dalilin zaman gida wanda wannan annoba ya janyo, ya samu raguwar kudin shiga a saboda karancin samun tallace-tallace daga kamfanoni da kananan 'yan kasuwa.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Facebook Ya Kara Sabon Alamar 'Care'"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka