Taskar Ahmad Bala

Gwagwarmayar yau da kullum a rayuwar ma'abocin Fasaha da Kirkire-kirkiren Zamani

Bayani Game Da Shirin Tallafin MSME SURVIVAL FUND

Wallafan September 28, 2020. 6:03pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Intanet da Yanar gizo

MSME SURVIVAL FUND shiri ne wanda gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi don tallafa wa matsakaita da kananan kamfanoni da masa'na'antu har ma da masu kananan sana'o'in hannu, domin farfado da su da kuma basu tallafi wajen ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin su, a sanadiyyar annobar cutar Korona. Kamar dai yadda taken shirin ya nuna, inda MSME ke nufin 'Micro Small and Medium Enterprises'.

Shirin na MSME SURVIVAL FUND shiri ne da gwamnatin ta bullo da shi ta karkashin ma'aikatar kula da masana'antu da cinikayya da zuba hannun jari ta kasa wato 'Federal Ministry of Industries, Trade and Investment' tare da hadin gwiwar SMEDAN, NASME, Bank of Industry, ITF da kuma MSME Clinic. Kuma shirin wani sashe ne na tsarin da gwamnatin tarayyan ta bullo da shi wanda ta sanya wa taken 'Nigeria Economic Sustainability Plan' inda ta ke niyyar tallafa wa 'yan kasuwa akalla miliyan 1.7 a kasar, ta hanyar kashe zunzurutun kudi har naira triliyon 2.3 wajen bayar da tallafi don ceto kasar daga shiga halin kakanikayi a sakamakon annobar ta korona.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/nigeria-market-rtx2m43j.jpg

Bangarorin Shirin na MSME SURVIVAL FUND

Shirin na da bangarori guda uku kamar haka:

  1. Payroll Support
  2. Guaranteed Offtake
  3. MSME Grant

Bangare na farko wato "Payroll Support" shi ne na kamfanonin da suka gaza biyan ma'aikatan su albashi a tsawon watanni 3 da suka gabata. tallafin albashin zai kasance daga N30,000 zuwa N50,000.

Bangare na biyu wato "MSME Grant" shi ne na masana'antu, wanda suke bukatan tallafin kudi wajen ci gaba da aiyukan sarrafa hajojin su.

Sai kuma bangare na uku wato "Guaranteed Offtake" wanda shi ne na masu kanana da matsakaitan kasuwanci.

Ga matakan da za a bi domin cin moriyar wannnan tallafi:

1. Domin shiga cikin shirin, da farko sai an ziyarci shafin nan: https://www.survivalfund.ng ko kuma https://www.survivalfundapplication.com

2. Da zaran an budo shafin za a ga wani maballi a sama inda aka rubuta "Start Here", sai a latsa shi. Za a ga ya budo shafin da aka jero bangarorin da shirin ke kunshe da shi.

3. A latsa daya daga cikin bangarorin da ake ganin ya dace da kasuwancin da ake yi.

4. Daga nan za a ga matakan da za a bi da kuma fom din da za a cike, dai-dai da nau'in bangaren da aka zaba.

A halin yanzu an bude bangare na farko wato "Payroll Support" Don haka masu bukata za su iya yin rajista kafin ranar Alhamis 15 ga watan Oktoba na wannan shekarar ta 2020.

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/1/business-in-nigeria-768x432.jpg

Ga matakai guda 4 da ake bi don yin rajistan:

  1. Personal Registration
  2. Account Activation
  3. Organisation Registration
  4. Complete the payroll support application

A matakin farko wato "Personal Registration" Za a ga fom mai dauke da guraben cikewan kaman na Suna, Sunan Mahaifi, Adireshin Email, Lamban waya, Jinsi, Ranar haihuwa da sauran su.

A mataki na biyu kuma, wato "Account activation" za su aiko maka da wasu lambobin tabbaci ('activation code') zuwa lamban wayan da ka saka a matakin farko.

A mataki na uku kuma wato "Organisation registration" za a bukaci yin login domin shigar da bayanai game da kamfanin ka, tare da lambobin rajistan ka na CAC, da kuma lambobin rajista na SMEDAN, da Tax ID da kuma lamban account na banki da dai sauran su.

A matakin karshe kuma za a samu sakon Email wanda ke kunshe da bayanan abubuwan da ake bukata don kammala rajistan. Abubuwan sun hada da sunayen kimanin ma'aikatan kamfanin ka 10, da shaidar biyan su albashi a baya, da kuma sauran 'documents'.

Da zaran an kammala duk wadannan matakai guda 4 to an kammala shiga cikin shirin kenan. Sai kuma a saurari dacewa da samun tallafin kudin.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 6 a kan "Bayani Game Da Shirin Tallafin MSME SURVIVAL FUND"


Babu hoto29-09-2020
Abdurraheem Muhammad

Allah ya saka da alheri Mal Ahmad yakara Basira


Babu hoto29-09-2020
Jamila Isah

Rubuta sharhin a nan...


Babu hoto29-09-2020
Abubakar

Abubakar suwidi


Babu hoto29-09-2020
Khadijah suleiman

Mungode


Babu hoto29-09-2020
Shamsuddeen A Jibrin

Mungode da wannan karin bayani amma mu da bamu kamfani Sai sana'ar ya ya tsarin yake kuma yaushe za'a bude namu.


Babu hoto29-09-2020
Assani Imam

Gaskiya Engr. Ahmad muna godiya sosai da wannan qarin bayani, Allah ya qara basira

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Ahmad matashin injiniya ne daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria, kuma kwararre wajen gina manhajar yanargizo. A gwagwarmayar sa na ganin ya bayar da gudun mawa ga al'ummar sa a wannan fanni, ya kirkiri manhajojin yanargizo da dama, daga cikin su akwai manhajar ZamaniWeb. Mutum ne mai son koyo da kuma koyarwa a kan duk wani abu da ya danganci fasaha da kirkire-kirkire. Ku biyo shi: @abzariya


Ko Kun San...?

ZamaniWeb manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato website, a saukake, cikin harshen Hausa. Irin sa na farko wanda aka yi shi cikin harshen gida na Afrika. Shiga yanzu: ZamaniWeb.ComKasidu Masu Alaka